’Yan mata 15 sun yi arba da ajali a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku a kauyen Dandeji da ke Karamar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.
Lamarin wanda ya auku a safiyar wannan Talatar bayanai sun ce kwale-kwalen ya kife da ’yan matan da ke kan hanyarsu ce ta zuwa diban itace.
- Kotu ta dage shari’ar neman tube rawanin Sarkin Zazzau
- An kama tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan
Kamar yadda wakilinmu ya ruwaito daga wani ganau da lamarin ya faru a kan idonsa, ya ce mahaya kwale-kwalen wadanda dukkansu ’yan mata ne aun haura mutum 40 a lokacin da lamarin ya faru.
Wani mazauni yankin mai suna Muhammad Ibrahim, ya ce gwanayen ninkaya sun tsamo gawarwakin mutum 15 yayin da ake ci gaba nutso wajen lalubo sauran da lamarin ya rutsa da su.
Shugaban Karamar Hukumar Shagari, Aliyu Abubakar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an soma shirye-shiryen gudanar da jana’izar mamatan da mai yanke kauna ta yi wa halinta.
Ana iya tuna cewa, a shekarar biyun da suka gabata, hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 33 wadanda mafi akasari mata ne da kananan yara a kauyukan Ginga da Gidan Magana a jihar ta Sakkwato.
Kazalika, wasu mabiya darikar Tijjaniya sun riga mu gidan gaskiya a irin wannan yanayi yayin bukukuwan Maulidi a bana.