Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Usman, da wasu mambobin majalisar biyar sun yi murabus a ranar Alhamis.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wasikar da Sakataren Majalisar, Shehu Muhammad-Yauri, ya rattaba wa hannu wadda aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
- NAJERIYA A YAU: Yadda aka tsefe manufofin manyan ’yan takarar Shubancin Najeriya a zaben 2023
- Malamai da tsofaffin soji ba sa kwazo a jagoranci —Obasanjo
“Manyan jami’an Majalisar shida, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar sun yi murabus daga mukamansu,” in ji wasikar.
Wasikar ta nuna 20 daga cikin mambobi 24 da majalisar ke da su suka sanya hannu a wasikar ajiye mukamamn takwarorin nasu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa babu wani cikakken bayani kan dalilin yin murabus din da jami’an suka yi.
(NAN)