Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano su tara sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.
Mai magana da yawun majalisar, Uba Abdullahi ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
- An yi gwanjon rigar kwallon Maradona kan Naira biliyan 3.6
- Saudiyya ta kama wasu ’yan Najeriya da suka daga hotunan ’yan siyasa a Harami
Ya ce mambobin sun aike da wasika ga Kakakin Majalisar inda suka sanar da shi batun sauya shekar tasu.
A cewar Uba Abdullahi, wasu daga cikin dalilan da suka bayar sun hada da rikicin da ake fama da shi a cikin jam’iyyar tasu a matakan jiha da ma tarayya.
’Yan majalisar da suka sauya shekar sun hada da Isyaku Ali Danja (Gezawa), Umar Musa Gama (Nassarawa), Aminu Sa’adu Ungogo (Ungogo), Lawan Hussain Chediyar ’Yan Gurasa (Dala) da kuma Tukur Muhammad (Fagge).
Sauran sun hada da Mu’azzam El-Yakub (Dawakin Kudu), Garba Shehu Fammar (Kibiya), Abubakar Uba Galadima (Bebeji) da kuma Mudassir Ibrahim Zawaciki (Kumbotso).
Idan za a iya tunawa, a ranar 29 ga watan Afrilu ce Majalisar ta sanar da sauya shekar mamba mai wakiltar mazabar Birni da Kewaye, Salisu Gwangwazo daga PDP zuwa APC, shi ma saboda rikicin cikin gida a PDPn.