’Yan Majalisar Wakilai sun koka cewa yoyon da kwanon ginin zauren majalisar yake yi yana barazana ga rayuwarsu.
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Honorabul Ndudi Elumelu, ya ce akwai babban hatsari idan mambobin majalisar suka ci gaba da zama a ginin, wanda ke fama da matsaloli.
- Ba za mu fallasa masu taimakon ’yan ta’adda —Malami
- Shehun Borno ya amince tsoffin ’yan Boko Haram su dawo cikin al’umma
Da yake gabatar da koken a lokacin zaman majalisar na ranar Lararba, Honorabul Elumelu ya yi kira da a gaggauta gyara matsalar yoyon kwanon da ma sauran wuraren da ke da matsala a gine-ginen Majalisar.
“Mai girma Shugaban Majalisa idan ka duba ruwa ne ya kewaye mu saboda yoyon kwanon ginin nan; Ina cikin damuwa saboda idan ba a gaggauta daukar matakin magance matsalar ba, to komai zai iya faruwa da rayuwarmu.
“Dubi yadda ma’aikata ke ta ta faman kwashe ruwan da ke malala da zauren Majalisa, wanda kuma barazana ce ga halartar zaman Majalsiar na yau da kullum. Ya kamata dai a yi wani abu a kan wannan matsala,” inji shi.
Bayan jawabin na Elumelu, Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce maganar na da muhimmanci matuka.
An jima dai rufin Majalisar Tarayya yana yoyo, inda ake ganin ruwa yana malale sassan ginin, wani lokaci sai an bi ta cikin ruwan ake wucewa.