✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan luwadi 5 sun shiga hannu a Nasarawa

Jami'an Sibil Difens sun cafke wasu matasa biyar bisa zargin aikata luwadi a Jihar Nasarawa.

An cafke wasu matasa su biyar bisa zargin aikata luwadi a Jihar Nasarawa.

Jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens sun cafke mutanen ne a kananan hukumomin Lafia da Doma na jihar.

Kakakin hukumar a jihar, DSC Jerry Victor ya ce dubun mutanen da ake zargi ta cika ne a wurare daban-daban da ke kananan hukumomin.

Ya ce daga cikin mutanen akwai dan shekara 17 da mai shekara 27 da kuma mutum uku da kowannensu shekarunsa 28.

Sanarwar da ya ce, “A yayin da aka titsiye su, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun yi shekaru suna yin luwadi, amma suka roki a yi musu afuwa.”

Sai dai ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a kotu domin ya zama darasi ga masu muguwar dabi’ar.

A cewarsa, kwamandan hukumar a jihar ya yi tir da mummunar dabi’ar sannan ya yi kira ga iyaye a fadin jihar da su sanya ido kan tarbiyya da halayyar ‘ya’yansu.