Wadansu da ake zargin masu safatar miyagun kwayoyi ne sun kashe wani jami’in Hukumar Yaki da Sha da kuma Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a Jihar Adamawa, Mistake Samuel wanda aka fi sank da Mbaka tare da raunana abokan aikinsa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta ce al’amari ya faru ne a kauyen Hilda na Karamar Hukumar Hong a lokacin da jami’an da ke kan hanyarsu ta zuwa Yola da wasu dillalan kwayoyi da suka kamo daga Karamar Hukumar Michika suka yi gamo da mashayan.
“Likita ya tabbatar da mutuwar daya daga cikin jami’an sakamakon harin sauran kuma na samun kulawar da ta dace, sannan Kwamishinan ’Yan Sanda ya ba da umarni a gudanar da bincike nan take”, inji Kakakin Rundundar, DSP Sulaiman Yahaya Nguroje.
Shaidu sun ce kasancewar ranar kasuwar garin ce, jami’amn na isa Hong sai wadanda aka kama din suka fara ihun neman taimako da cewa garkuwa da su aka yi.
Jin hakan ya sa jama’a taruwa a kan motar kuma duk da jami’an sun nuna shaidar katin wajen aiki amma abin ya ci tura.
Nan take wasu suka dauko adduna suka yi ta saran su har suka kashe daya daga cikinsu suka kuma kona gawarsa tare da raunana sauran.
“Yanzu dai ba a san inda wadanda ake zarzin suke ba,” inji wadanda al’amarin ya faru a gabansu.
Zuwa lokacin hada rohoton nan Shugaban NDLEA na Jihar Adamawa ya yi tafiya, sai dai wata majiya mai karfi a hukumar ta bayyana faruwar a in a matsayin abin da hankali ba zai dauka ba.
Ko da Aminiya ta tuntubi dan uwan mamacin, Ayuba Burma, ya ce marigayin ya kasance mutumin kirki sannan ya bukaci jami’an tsaro da su dage wajen gano wadanda ke da hannu a ciki.