A cigaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya da yanzu haka yake gudana a Brazil, rahotanni sun nuna ’yan kwallon Najeriya Super Eagles sun bukaci gwamnatin tarayya ta ba kowannensu Dala dubu 75 kwatankwacin Naira miliyan 12 a matsayin kasonsu daga tallafin da Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta ba Najeriya saboda cancantar da ta yi na halartar gasar.
Kamar yadda rahoton ya nuna, ’yan kwallon sun gabatar da bukatar hakan ne a lokacin da Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Dabid Mark ya kai musu ziyara a ranar Juma’ar da ta gabata watau tun kafin Najeriya ta buga wasanta na farko da Iran a ranar Litinin.
Sannan ’yan kwallon sun bukaci gwamnatin tarayya ta canza musu Otel din da suke zaune mai suna bictorious Concept Hotel da ke garin Campinas zuwa wani wanda ya fi shi tsari da kuma kusa da inda suke buga wasanni.
Sun ce otel din da aka kama musu ya yi nisa daga inda suke yin wasanni kuma hasalima ma yana bayan gari ne al’amarin da ya sa suka kasance a matsayin saniyar ware da sauran kasashen da suke zaune a cikin gari.
A nasa bangaren Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Dabid Mark ya ce ya saurari bukatunsu da kunnen basira kuma ya yi alkawarin gabatar da koken nasu ga gwamnati don ganin an share musu hawaye.
Sai dai ya hore su da su yi kokarin ganin sun daukaka sunan Najeriya a idon duniya a yayin gasar ta hanyar tabuka abin a-zo-a-gani.
Hukumar NFF dai ta bayyana alawus din Dala dubu 10 kwatankwacin Naira miliyan 1 da dubu 600 a matsayin kudin da kowane dan kwallon Najeriya zai samu idan sun yi nasara a kowane wasa.
Hukumar FIFA ta ba Najeriya kason Dala miliyan 9 daidai da Naira biliyan 1 da dubu 400 a matsayin kasonta a kokarin da ta yi na halartar gasar cin kofin duniya a Brazil. Daga cikin wannan kaso ne ’yan kwallon suke bukatar su ma a ba su Naira miliyan 12 kowannensu a matsayin nasu kason tun kafin a fara gasar.
Sai dai ya zuwa yanzu babu tabbacin ko an biya ’yan kwallon wannan kudi ganin cewa a gobe Asabar ne Najeriya za ta yi wasanta karo na biyu da kasar Bosniya Herzegobina bayan Iran ta rike mata wuya inda aka tashi babu ci a wasanta na farko.
’Yan kwallon Super Eagles na bukatar a ba kowannensu Naira miliyan 12
A cigaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya da yanzu haka yake gudana a Brazil, rahotanni sun nuna ’yan kwallon Najeriya Super Eagles sun…