A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala wasan cin kofin shugaban ‘yan sandan Kudancin Kaduna AC Ibrahim Abdullahi bayan an kwashe kwanaki tara ana fafatawa.
Wasan, wanda aka tashi kunnen doki tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Samaru United da suka fito daga karamar hukumar Zangon Kataf da kuma Golden Balley FC daga karamar hukumar Jema’a, ya samu halartar matasa daga yankin Kudancin Kaduna da aka dade ba a ga irinsa ba.
Bayan an tashi daga wasan ne aka yi bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti) inda Samaru Kataf suka ci duka kwallayensu yayinda su kuma Golden Balley suka zubar da bugun farko.
A cikin jawabin da ya gudanar bayan kammala wasan, AC Ibrahim Abdullahi ya bayyana farin cikinsa da yadda wasan ya gudana cikin kwanciyar hankali ba hayaniya sannan ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga ‘yan kwallon da sauran matasan da suka hallara a filin cewa su zama masu fadi tashi, kada su karaya a kan komai na rayuwa. A karshe ya yi kira ga matasa da su daina jiran sai sun samu aikin gwamnati idan sun gama makaranta maimakon haka su rika neman sana’ar yi.
Shi ma Kocin Samaru United, Jacob Dogo ya shaidawa ‘yan jarida cewa wannan abin alfahari ne a wajensa kasantuwar bai taba cin wani kofi a garin Kafanchan ba sai a wannan karon kuma ya ji dadi da irin hadin kan da ya samu daga wajen ’yan wasansa. Ya kara da cewa hadin kai a tsakanin Musulmi da Kirista shi ne babban darasin wannan wasa saboda a cikin ‘yan wasansa akwai musulmi kamar yadda a cikin ‘yan wasan abokan hamayyarsa ma akwai kirista.
kungiyar kwallon kafa ta Golden Balley Kafanchan ce ta zo na biyu yayinda kungiyar kwallon kafa ta Unguwar Rimi FC wacce ita ma ta fito daga karamar hukumar Zangon Kataf ta zo na uku kuma kowanne ya samu kyaututtuka.
‘Yan Kwallon Samaru sun lashe gasar shugaban ‘Yan sandan Kudancin Kaduna
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala wasan cin kofin shugaban ‘yan sandan Kudancin Kaduna AC Ibrahim Abdullahi bayan an kwashe kwanaki tara…