✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon da ke hada karatu da kwallo a Turai

Rahoton da kafar labarai ta Legit.ng ta kalato ya bayyana yadda wadansu ’yan kwallon kafa biyar  da suke amfani da damar da suka samu wajen…

Rahoton da kafar labarai ta Legit.ng ta kalato ya bayyana yadda wadansu ’yan kwallon kafa biyar  da suke amfani da damar da suka samu wajen hada harkar kwallon kafa da kuma yin karatu a jami’o’in Turai.

Daga cikin ’yan kwallon akwai Wilfred Ndidi, dan kwallon Super Eagles da yake wasa a kulob din Leicester City na Ingila.  A kwanakin baya Ndidi ya bayyana wa duniya a kafar sadarwarsa cewa ya shiga wata jami’a da ke Ingila inda yake karatun digiri a fannin yawon shakatawa da kasuwanci. Dan kwallon ya ce ya yi haka ne domin idan ya yi ritaya daga buga kwallo ya samu abin dafawa.

Na biyu shi ne Fikayo Tomori  dan asalin Najeriya da yanzu haka ke kwallo a kulob din Chelsea na Ingila. Tomori shi ma ya bayyana cewa tuni ya shiga wata jami’a a Ingila don ya samu digiri. Dan kwallon ya ce saboda irin matsalolin da wadansu ’yan kwallo ke fuskanta idan sun yi ritaya a kwallo ne, ya sa ya yanke shawarar yin karatu a jami’a.  “Harkar kwallo ba ta da tabbas, akwai jin rauni sannan akwai tsufa, idan daya daga cikin wadannan abubuwa biyu ya same ka, sannan ba ka yi karatu ba, to akwai matsala,” inji Tomori.

Na uku daga ’yan wallon da suka rungumi karatu a jami’a shi ne Juan Mata, dan asalin Spain da yanzu haka yake wasa a kulob din Manchester United na Ingila, rahoto ya nuna ya mallaki digiri biyu a bangarori daban-daban a wata jami’a da ke Spain. Ya samu digiri a fannin aikin jarida da kuma fannin wasanni da fannin kudi.  Juan Mata dan shekara 31 alamu sun nuna zai rungumi harkar horarwa da zarar ya yi ritaya a kwallo.

Na hudu shi ne Giorgio Chellini, Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Italiya da kuma kulob din Jubentus na Italiya yana daya daga cikin ’yan kwallon da suka mallaki digiri a wata jami’a da ke Italiya.

Hasali ma yana daga cikin daliban da suka samu sakamako mafi kyau. Dan kwallon ya hada kwallo da karatu ne saboda tunkarar aikin horarwa da zarar ya daina buga kwallon kafa.

Na biyar shi ne dan kasar Beljiyam, Romelu Lukaku.  Lukaku wanda ya yi kwallo a kulob da dama da suka hada da Eberton da Manchester United dukkansu a Ingila, yanzu haka yana wasa ne a kulob din Inter Milan da ke Italiya.

Rahoto ya nuna dan kwallon ya mallaki digiri a fannin yawon bude-ido da kuma hulda da jama’a.  Saboda fasaharsa yana jin harsuna masu yawa.  Daga cikin harsunan da Lukaku yake ji akwai Ingilishi da Sifaniyanci da na Holland da Faransanci da harshen Fotugal da Jamusanci da kuma na Swahili.