✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan kwallo 20 da suka buga wasa fiye da 100 a Gasar Zakarun Turai

Silva shi ne na biyu da ya buga wasa na 100 a Gasar Zakarun Turai a kakar 2022/23.

’Yan wasa arba’in da bakwai ne suka buga wasanni 100 ko fiye a Gasar Zakarun Turai ta Champions League tsawon shekaru.

Aminiya ta ruwaito yadda a Talatar da ta gaba aka soma buga wasanni na hudu-hudu na cikin rukuni a Gasar Zakarun Turai ta bana.

Daga cikin wasanni da aka fafata, Chelsea ta doke AC Milan 2-0 a wasan rukuni na biyar da suka a barje gumi a San Siro.

Hakan ya sa Chelsea wadda ta doke kungiyar Italiya 5-0 gida da waje a bana ta dare mataki na daya a kan teburin da maki bakwai.

Red Bull Salzsburg ce ta biyu da maki shida, sai Milan da Dinamo Zagreb da kowacce tana da maki hurhudu.

Da wannan wasan, mai tsaron bayan Chelsea Thiago Silva wanda ya buga karawar ya kuma zama na baya-bayan nan da ya yi wasa na 100 a Gasar Zakarun Turai.

Hakan ya sa ya zama na 47 da suka buga wasanni 100 zuwa sama a babbar gasar tamaula ta Turai a tarihi.

Mai tsaron bayan Brazil, ya yi wasan farko 20 a AC Miilan, wanda ya fara buga gasar ranar 12 ga watan Satumbar 2009 da Milan ta ci Merseille 2-1.

Silva shi ne na biyu da ya buga wasa na 100 a Gasar Zakarun Turai a kakar 2022/23, bayan Angel Di Maria na Juventus a wasa na biyu a cikin rukuni a bana.

Ga jerin ’yan wasa 20 da suka yi wasa sama da 100 a Gasar Zakarun Turai:

183 Cristiano Ronaldo (Manchester United 59, Real Madrid 101, Juventus 23)

177 Iker Casillas (Real Madrid 150, Porto 27)

159 Lionel Messi (Barcelona 149, Paris Saint-Germain 10)

151 Xavi Hernández (Barcelona)

145 Karim Benzema (Lyon 19, Real Madrid 126)

142 Raúl González (Real Madrid 130, Schalke 12)

141 Ryan Giggs (Manchester United)

136 Thomas Müller (Bayern München)

133 Sergio Ramos (Real Madrid 129, Paris Saint-Germain 4)

131 Manuel Neuer (Schalke 22, Bayern München 109)

131 Toni Kroos (Bayern München 41, Real Madrid 90)

130 Andrés Iniesta (Barcelona)

128 Sergio Busquets (Barcelona)

127 Gerard Piqué (Manchester United 4, Barcelona 123)

125 Clarence Seedorf (Ajax 11, Real Madrid 25, AC Milan 89)

124 Gianluigi Buffon (Parma 6, Juventus 113, Paris Saint-Germain 5)

124 Paul Scholes (Manchester United)

124 Zlatan Ibrahimović (Ajax 19, Juventus 19, Inter 22, Barcelona 10, AC Milan 20, Paris Saint-Germain 33, Manchester United 1)

120 Roberto Carlos (Real Madrid 107, Fenerbahçe 13)

119 Xabi Alonso (Real Sociedad 8, Liverpool 39, Real Madrid 47, Bayern München 25)