Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta ce za ta gudanar da zanga-zanga a ranakun 26 da 27 na watan Yulin 2022 don nuna goyon bayanta ga yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU).
Shugaban NLC na kasa, Kwamared Ayuba Wabba ne ya bayyana haka a cikin wata wasika da ya sa wa hannu tare da Sakataren kungiyar, Mista Emmanuel Ugboaja, dauke da kwanan watan 15 ga watan Yuli, kuma aka raba wa shugabannin kungiyar na jihohi.
- Jirgin saman Ukraine da ke dauke da makamai ya yi hatsari a Girka
- Likitoci sun gano tsabar kudi da batura da kusoshi 233 a cikin mutum
Jami’o’in gwamnati a Najeriya dai sun kasance a rufe tsawon wata biyar, sakamakon yajin aikin da ASUU da sauran kungiyoyin ma’aikatan makarantun ke ci gaba da yi.
Suna yajin aikin ne saboda alkawuran da suka ce gwamnati ta gaza cika musu, da suka shafi albashi da wasu kudaden alawus-alawus.
A cewar Kwamared Ayuba, daukar matakin ya zo daidai da shawarar Kwamitin Zartarwar uwar kungiyar na kasa, wanda ya gudanar da taro ranar 30 ga watan Yuni.
Kungiyar kwadagon dai ta ce za ta yi zanga-zangar ce don tilasta wa Gwamnatin Tarayya da na jihohi su yi abin da ya dace don kawo karshen yajin aikin.
Wabba ya ce, “Mun shirya yin wannan zanga-zangar ce don ganin ’ya’yanmu sun samu sun koma makarantun gwamnati da kuma inganta harkar ilimi.
“Za a yi wannan zanga-zangar ce a ranakun 26 da 27 a dukkan jihohin Najeriya da kuma Abuja.
“Wuraren da za a fara zanga-zangar su ne Sakatariyar NLC da ke jihohin da kuma ta kasa da ke Gidan ’Yan Kwadago a Abuja,” inji wasikar.