Ana zargin wasu ’yan kwadago da kashe wani manomi mai suna Hussaini Aliyu a gonar shi, tare da jefa gawar a rijiya.
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta rawaito cewa lamarin ya faru ke kusa da gonarsa a unguwar Jeida da ke Kuje a Abuja.
- Sojoji sun tsinto guda daga ’yan matan Chibok da aka sace da jaririnta
- WHO za ta sauya wa cutar Kyandar Biri suna
Wakilanmu sun rawaito cewa manomin ya bace a gona tasa tun ranar 2 ga watan Yuni, sai dai bayan bincike mai tsanani aka gano shi da alamar an kashe shi kana aka wulla gawarsa a rijiya.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilanmu ta wayar tarho, Mataimakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan birnin, ASP Oduniyi Omotayo, ya ce an kamo wadanda ake zargin a unguwar Kabusa a hanyar su ta tahowa Kano da shanun margayin.
Kazalika Omatayo ya ce har yanzu rundunar na kan bincike, kuma da zarar ta kamala za ta sanar da al’umma halin da ake ciki.
Haka zalika ya ce tun da fari dan uwan manoin ne ya kai rahoton bacewarsa ranar hudu ga watan Yuni, in da ya bayyana cewa bai dawo daga gonarsa ba tun ranar biyu ga watan Yuni da ya tafi can.
“Yana sanar da mu jami’anmu suka shiga bincike wanda har ya kai ga kamo ma’aikatan manomin biyu daga cikin wadanda ake zargin a Kabusa suna kan hanyar tserewa zuwa Jihar Kano”, inji Kakakin rundunar.
Bayan shanun dai an gano tumaki 40, da Akuyoyi shida wadanda ma’aikatan da ake zargin sun kashe manomin suka kora daga gonarsa.