Sabon fada ya barke tsakanin kungiyoyin asiri a Jihar Edo, musamman mazabar Edo ta Kudu, inda kungiyoyin suka mamaye kananan hukumomi uku.
Tun bayan rikicin da ya barke a makon jiya, mutum sama da 20 da ’yan sanda uku ciki har da Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda, wanda ’yan bindiga suka harba a yankin Upper Sakpoba.
- An cafke barayin shanu biyu a Edo
- Matsalar tsaro: Za a samar da rundunar hadaka a Kudu maso Yamma
- An cafke ‘yan kungiyar asiri 54 a Akwa Ibom
- An damke ‘yan fashi da kungiyar asiri 17 a Binuwai
Rahotanni sun bayyana cewa an dauki tsawon lokaci ana fada tsakanin ’yan kungiyar asiri a jihar wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.
An gano cewa ’yan kungiyar asiri daban-daban a jihar na fadace-fadace ba dare ba rana, wanda ya sa mutane da dama shiga zulumi.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan kungiyar asirin ta sace-sacen kayan mutane, suna fasa manyan shaguna da ofisoshin ’yan sanda suna awon gaba da bindigogi da harsasai.
Bincike ya sake nuna cewa wasu daga cikinsu ne suka saki fursunoni daga gidan yari a jihar a loacin zanga-zangar #EndSARS.
Kwamishanan ’Yan Sanda jihar, Johnson Kokumo, ya ce jami’ansa na kokarin ganin sun dawo da zaman lafiya kamar yadda yake a jihar.
Sannan ya kara da cewa ofisoshin ’yan sanda uku da ke kan hanyar Sokponba an kone su tare da lalata wasu daga cikin motocinsu na sintiri a Benin, babban birnin jihar.