✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kungiyar asiri 27 sun shiga hannu a Nasarawa

Hukumar Tsaron ta Farin Kaya (NSCDC), ta kama wasu mutane 27 kan zargin su da zama mambobin kungiyoyin asiri a Jihar Nasarawa.

Hukumar Tsaron ta Farin Kaya (NSCDC), ta kama wasu mutane 27 kan zargin su da zama mambobin kungiyoyin asiri a Jihar Nasarawa.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin, Kwamandan NSCDC na jihar, Bappa Abbas Muhammed, ya ce an kashe wani mutum daya aka kuma sassari wasu da dama da adduna a rikicin kungiyoyin asiri.

Kwamandan na NSCDC ya du za a gurfanar da duk wadana suka shiga hannun a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka.

Da yake bayyana takaicinsa kan abin da ya faru, jami’in ya bayyana damuwa kan karuwar ayyukan kungiyoyin asiri a kananan hukumomi 13 da ke fadin jihar, musamman Lafiya, hedikwatar jihar.

Sai dai ya ce hukumar ta kaddamar da wani sabon aiki na musamman domin shawo kan matsalar.