’Yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu ’yan kasuwa a Kasuwar Kagara ta Karamar Hukumar Rafi a Jihar Neja, sun sako su bayan shafe wata uku a hannunsu.
Idan za a iya tunawa, ’yan bindigar sun farmarki Kasuwar Kagara ne a ranar 9 ga watan Satumba, 2021 inda suka yi awon gaba da akalla mutum 34.
- Najeriya A Yau: Za A Kashe Duk Wanda Ya Saci Mutum A Filato
- Najeriya A Yau: Za A Kashe Duk Wanda Ya Saci Mutum A Filato
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da kubutar ’yan kasuwar.
Ya ce, “Ragowar mutum 28 da suka hada da maza da mata, an sako su kuma tuni aka ceto ragowar mutum shida, an kuma sada su da iyalansu a ranar 5 ga watan Oktoba, 2021.”
Abiodun ya ce an kai mutanen da suka kubuta asibiti don ba su kulawar da ta dace kafin daga bisani a sada su da iyalansu.
Rahotannin sun bayyana cewa wasu mutane da aka tsare a Dajin Kango na kauyen Dangulbi a Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara, sun kubuta bayan maharan da suka sace su suka sake su a kan hanyar Kamfani-Doka da ke Birnin Gwari a Jihar Kaduna, bayan hare-haren da sojoji ke kai wa ’yan bindiga a Zamfara.