Kamfanin sarrafa siminti na BUA, ya zargi ’yan kasuwa da cewa su ne kanwa uwar gamin da suka sa farashinsa ya ki saukowa a Najeriya.
A cewar kamfanin, ’yan kasuwar ne suka hana farashin saukowa, duk kuwa da ragin kaso 10 cikin 100 da ya yi a kan farashin kowane buhu.
- ‘Rikicin Rasha da Ukraine zai kawo tsadar burodi a Najeriya’
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabuwar Dokar Zabe Za Ta Shafi Gudanar da Zaben Najeriya
Shugaban kamfanin, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u ne ya bayyana haka a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan da kammala ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja.
Ya ce tuni kamfanin nasa ya fara tattaunawa da sauran masu sarrafa simintin da nufin ganin an rage farashinsa a Najeriya.
Sai dai ya ce, “Muddin ba mu samu hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ba, to ba za a ga tasirin yunkurin namu ba.
“A zahirin gaskiya, mun yi tunanin bayan mun rage farashin simintinmu da N350, sauran kamfanoni za su bi sahunmu, amma sai suka ki.
“Mun kuma ga yadda farashin ya ci gaba da karuwa, lamarin da ya sa manya da kananan diloli kan samu ribar kusan N800 zuwa N1,000 a kan kowane buhu,” inji Abdussamad.