Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba wa ƙananan ’yan kasuwa da matsakaita su 9,403 a ƙananan hukumomin Biu da Hawul, tallafin Naira biliyan ɗaya.
Wannan tallafi na da nufin ƙarfafa kasuwanci, haɓaka tattalin arziƙi, da rage talauci a yankunan.
- Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina
- Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha
A Biu da Hawul, gwamnan ya raba Naira miliyan 560.3 ga ’yan kasuwa 5,603, inda kowane mutum ya samu Naira 100,000.
Hakazalika, ya raba Naira miliyan 439.7 ga matasa da magidanta 1,800 a Biu da kuma ’yan kasuwa 2,000 a Hawul.
Gwamna Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa da matasa don bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi.
Ya buƙaci waɗanda suka samu tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata, inda ya bayyana cewa hakan na daga cikin alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Har ila yau, ya umarci hukumar zuba jari ta Jihar Borno (BOSIMP) da ta tantance ƙarin matasa 2,000 marasa galihu domin su ma su amfana da tallafin a nan gaba.