✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwa da ke Arewa maso gabas sun bukaci tallafin gwamnati (2)

Mataimakin Shugaban kungiyar ’yan kasuwan yankin Arewa-maso-Gabas Alhaji Arma Ya’u Yahaya ya bukaci gwamnonin yankinsu da su tallafawa ‘yan kasuwa da suka fada cikin mawuyacin…

Mataimakin Shugaban kungiyar ’yan kasuwan yankin Arewa-maso-Gabas Alhaji Arma Ya’u Yahaya ya bukaci gwamnonin yankinsu da su tallafawa ‘yan kasuwa da suka fada cikin mawuyacin hali sakamakon tashe-tashen hankulan da ya gurgunta harkokin kasuwanci a shiyyar.

Shugaban ya bayyana haka ne kwanakin baya lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Bauchi. Da yake tofa albarcin bakinsa game da sabbin gwamnonin ya ce yana kira da “babbar murya ga gwamnonin jihohin Gombe da Adamawa da Taraba da Yobe da Barno da kuma Bauchi da su yi wa Allah su taimakawa ‘yan kasuwan wannan yankin domin da yawa daga cikinsu sun samu karayan arziki sakamakon rikicin Boko Haram,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa yana fatar gwamnati zata tallafawa ‘yan kasuwa da jari domin kowa yasan cewa idan mutum baya da jari to tabbas ba zai samu ci gaba a harkokin kasuwancinsa ba.
Daga karshe ya ce za su ci gaba da yin addu’oi na musamman ga sabbin shugabannin da aka zaba tun daga kan sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari har zuwa kan ‘yan majalisun tarayya da na jihohi.