Wasu daga cikin jarumai da sauran masu alaka da harkar fina-finan Hausa ta Kannywood sun bi sahun mutanen da suka yi suka a kan wasu hotuna da jaruma Rahama Sadau ta wallafa.
Da dama daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar ta Kannywood dai sun yi tir da jarumar, wasu ma har tsinuwa suka yi, ko dai kai-tsaye, ko kuma a kaikaice.
- Bude katafaren wajen hutu na Rahma Sadau ya jawo cece-ku-ce
- Abinda ke tsakanina da Rahma Sadau – Yaseen Auwal
Jarumar dai ta fito ta nemi afuwa bisa wannan lamari.
A ranar Litinin ne aka wayi gari da hotunan Rahama sanye da wasu tufafi masu nuna jikinta, wadanda suka jawo cece-kuce.
Cece-kuce
Mutane da dama sun yi ta sukar jarumar tare da yin Allah wadai, sannan a gefe daya kuma wasu suka fito suna kare ta.
Jim kadan da musayar yawun ne, sai aka samu bayyanar wani maudu’i mai suna #AssistantAllah, wanda masu kare ta suka fito da shi domin ci gaba da ba ta kariya.
Kazalika, an samu wani wanda har yanzu ba a san ko wane ne ba, da ya yi batanci ga Manzon Allah (S.A.W) a kasan hotunan.
Bayan wannan batancin da aka yi wa Manzon Allah ne Rahama Sadau ta fito ta nesanta kanta da lamarin ta kuma nemi afuwa, inda ta nuna cewa ba da yawunta aka yi batancin ba.
Duk da haka…
Da yake tsokaci a kan lamarin, mawaki Isa Ayagi cewa ya yi, “Hakika mutum yana ba da samfuri ne na tarbiyar da ya samu tun daga yanayin shigarsa. Don haka ba na mamaki ga shigar da jaruma Rahama Sadau ta yi.”
Daga nan sai darakta Ali Gumzak ya ce, “Ya ALLAH Ka tsare mu daga musifa da fitinar wannan gurbataccen zamani. Ka saka mu cikin ’yantattun bayinka nagari. Ka tsare mana imaninmu da hankalinmu. Ya Allah Ka karawa Annabi S.A.W salati da salami fil Jannat.”
Shi ma jarumi Sani Danja, wanda ya sanya wani bidiyo da a ciki wani malami ke cewa mutane ne shaidun Allah a ban kasa, ya rubuta cewa, “Allah Ka sa a mana shaida ta alheri a duniya da Lahira.”
Tsinuwa
Shi kuwa darakta Sheikh Isa Alolo tsinuwa ya yi, inda ya sanya wani hoton rubutu mai dauke da tsinuwa ga Rahama Sadau, sannan ya kara da cewa, “Fada ce ta Manzon Allah S.A.W. ya ce ku tsine musu in kun gansu”.
Fitaccen furodusa, Abdul Amart Mai Kwashewa, cewa ya yi, “Subhanallah! Subhanallah! Subhanallah! Allah mun tuba! Allah mun tuba! Allah mun tuba! Ya Allah kar Ka kama mu da laifukan wawayen cikinmu.”
A kasan rubutun kuma, Sadiya Kabala ta ce, “Amin summa amin.”
Shi ma darakta Sanusi Oscar 442 ya sanya wani hoton rubutu mai dauke da sakon cewa da wanda ya yi, da wanda ya janyo aka yi, Allah Ya tsine musu albarka, sannan ya kara a kasa cewa, “Ni ba ni da kamar masoyina Annabi Muhammadu. Ya fi uwata ya fi ubana ya fi komai nawa. Wanda duk ya taba shi, babu ni babu shi.”
Aminiya ta gano cewa da farko Oscar ya sanya hotunan da suka jawo cece-kucen kafin su janyo batancin, amma daga baya ya cire su.
Tsokacin Ali Nuhu
Ali Nuhu, wanda shi ne asalin uban gidan jarumar, ya wallafa a shafinsa cewa, “Ya Allah Ka sa mu cika da imani. Ka sa mu nisanci duk wani abu da zai zama sanadiyyar jawo mana fushinka. Ya Allah Kai ke yin yadda ka so da bayinka. Allah Ka shirye mu da duk wani wanda yake da niyyar shiryuwa. Ka hane mu taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji. Ya Allah Ka ba mu ikon fahimtar nasiha ko da daga bakin ’ya’yan da muka haifa ne ballantana abokan zama, magabata da abokan sana’a da masoya na gaske albarkacin fiyayyen halitta Muhammad Rasulillah S.A.W. Allah yadda Ka raba mu da iyayenmu lafiya, Ka sa mu gama da duniya lafiya. Mu zama ababen kwantance nagari.”
A kasan rubutun, Abba el-Mustapha da Malam Ibrahim Yala suka amsa suna masu cewa amin.
Shi ma matashin furodusa, Alhaji Khalid Yusuf, wanda aka fi sani da Kherleedo, cewa ya yi, “Na rantse da Ubangijin da ya aiko Annabi Musa da Attaura sai kinga bala’i! Ta dalilinki aka taba wanda Allah Ya fi so, shi kanshi hotan da kika yi masifa ne ga rayuwarki ballantana ta dalilinsa an taba wanda Ya fi matsayi, matsayi.”
Sannan a wani sakon da ya fitar, jaruma Hafsat Idris ta yi magana, inda ta ce, “Gaskiya ne.”
Shi ma jarumi Abdul M. Shareef ya ce, “Tir da hali irin naki, Rahama.”
Alhaji Sheshe cewa ya yi, “Ba na goyon bayan bayyana fasikanci da tozarta addinin Allah ta hanyar bayyana tsiraici. Annabi S.A.W ya ce akwai wasu mutane ’yan wuta ne za su zo nan gaba. Amma ban gansu ba,” In ji manzonmu.
A cikinsu akwai (Kasiyatun Ariyatun) wasu mata da za su rika yin shiga ga kaya a jikinsu, amma kana kallon surar jikinsu kamar tsirara suke. In ji Annabi S.A.W wadannan matan ko kamshin Aljannah ba za su ji ba. Haka Annabi S.A.W ya ci gaba da cewa idan mun gansu mu tsine musu tunda Allah S.W.T Ya tsine musu.”
Shi ma furodusa Abubakar Bashir Maishadda cewa ya yi, “A labarin matan da suka daukaka a Kannywood suka samu kudi wallahi babu ke a tarihinsu. Ba kya amfanar da Kannywood da komai in ban da ki rika jawo mana masifa.
Shi ma Adam A. Zango cewa, “Allah Ka shirye ta idan ta yi taubatan nasuhu. Idan ba mai shiriya ba ce, Allah Ka la’ance ta.”
Shi ma fitaccen daraktan nan kuma jarumi a masana’antar, Falalu Dorayi ya ce yin shiru yayin da aka aikata wata barna, ita ma barna ce.
“Nasiha da jan hankali ba da tozarci ba, ita ce hanya mafi kyau musulmi ya yi wa dan uwansa musulmi nasiha a kan wata barna da ya ga yana aikatawa.
“Ita dai dabi’ar shigar banza nema take ta zama ruwan dare a al’ummarmu.
“Mace tana da daraja ga rayuwarta da ta al’ummarta ne, dan haka mu tashi wajen nusar dasu kunyarsu da mutuncinsu, domin gyara ‘ya’yanmu masu zuwa a gaba”, a cewar Dorayi.
Aminiya ta kuma ci karo da wasu hotunan bidiyo, inda jarumai irinsu Malam Ibrahim Sharukhan suke mata martani.