An yi waje da kungiyar kwallon kafa ta Olympique Lyon da kuma Paris FC da ke taka leda a aji na biyu na Gasar Kasar Cin Kofin Kasar Faransa (French Cup).
A ranar Litinin ne Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar Faransa ta zartar da hukuncin sakamakon shiga filin wasa da magoya baya suke yi a lokacin da ake tsaka da yin wasan.
- Najeriya A Yau: Sakacin gwamnati ne silar kai hari a makarantu A 2021
- Yadda ake magance yamutsewar fata a lokacin sanyi
Lamarin ya faru ne a ranar 17 ga watan Disamba, 2021 inda magoya bayan suka kaure da fada, wanda hakan ya sa a dakatar da wasan.
An ci tarar kungiyar Paris FC kudi Yuro 10,000 tare da hana ta amfani da filin wasanta a wasanni biyar da za su yi a gaba.
Am kuma dakatar da magoya bayan Lyon daga shiga kallon wasa har zuwa karshen kakar wasanni ta bana tare da cin kungiyar tarar kudi Yuro 52,000.
Kazalika, an dakatar da Lyon fafatawa a Gasar Kofin French Cup a shekara mai zuwa.
Kwallon kafa a kasar Faransa na fuskantar barazana daga magoya baya, musamman a wannan kakar wasanni ta bana.