✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kaduna sun yi wa El-Rufai raddi kan dawo da kulle

Gwamna Nasir El-rufa’i ya ce akwai yiwuwar sake kakaba dokar kulle a jihar Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-rufa’i ya ce akwai yiwuwar Jihar ta sake kakaba dokar kulle saboda yadda yawan sabbin masu kamuwa da COVID-19 ke hauhawa a ‘yan makonnin nan.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Sashen Hausa na BBC ya yu da shi a ranar Talata kan matakan da jihar take dauka don dakile yaduwar cutar a jihar.

Jihar Kaduna ta shafe sama da watanni uku a kulle a kokarinta na dakile yaduwar annobar.

El-Rufa’i ya ce, “Duk matakan da muka shimfida na kariya domin mutane su bi wajen kare kansu ba su bi.

“Idan ka je masallatai ranar Juma’a ka ga yadda mutane ke cudanya da juna za ka san cewa lallai muna cikin hadari.

“Mun ce mutane sun rika saka takunkumin rufe fuska wanda shi ne zai kare mutum daga kamuwa da cutar da kuma yada wa wasu amma ba sa sakawa.

“Za a tare mutum a hanya a ce ina takunkuminsa sai ya zaro a aljihu amma ba zai yi amfani da shi ba.

“Yanzu haka shirin da muke shi ne watakila mu sake rufe jihar don kada lamarin ya zo ya fi karfinmu”, inji El-Rufa’i.

— ‘Gara ka yi bara da ranka da ka mutu’

Da aka tambayi gwamnan kan halin matsin da sake kakaba kullen zai jefa jama’a musamman ‘yan kasuwa da yanzu wasunsu suka koma bara saboda kulle musu kasuwanni, ya ce a matsayinshi na wadanda aka zaba domin su kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu, ba za su yarda su jefa su a hallaka ba.

“Mun ji ‘yan kasuwa suna bara saboda matsin da suka shiga, amma ai gara ka yi bara kana da rai da ka mutu.

“Yanzu haka akwai tsare-tsaren da muka yi domin tallafa wa ‘yan kasuwar in komai ya koma daidai, amma yanzu dole ne mutane su hakura su ci gaba da bin wadannan matakan”, in ji El-rufa’i.


‘A shawarci kwararru’

To sai dai jama’ar jihar ciki har da ‘yan kasuwa da masu sharhi sun fara mayar da martani inda suke cewa sake kulle jihar zai iya jefa mutane cikin mawuyacin hali.

Malam Kabiru Danladi Lawanti, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya ce kamata ya yi ‘yan siyasa su rika shawara da kwararru kafin su dauki kowane irin mataki.

Ya ce, “Yan siyasa su yi siyasarsu, amma idan abu ya shafi lafiya ko rayuwar al’umma, kamata ya yi su ji shawarar kwararru musamman masana halayyar dan Adam, masana kiwon lafiya da ma tattalin arziki.

“Idan ka yi la’akari da alkaluman mutanen da suke kamuwa da cutar a Kaduna da yawan al’ummar jihar za ka ga cewa matakin da ake kokarin dauka na kara rufe gari bai dace da abun da yake a zahiri ba.

“Ba za ka rufe mutane sama da mutum miliyan biyar a kan wata cuta da har yanzu ba ta kashe mutum 200 gabadaya ba a jihar.

“Hakan ba abun da zai yi sai kara jefa mutane a cikin kangi saboda yanzu haka ma akwai gidajen da ke shafe kwanaki uku zuwa hudu ba su dora tukunya ba” inji  Malam Kabiru.

Mai sharhin wanda kuma malami ne Sashen Koyar da Aikin Jarida na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya shawarci gwamnan da sauran shugabanni da su rika saka tausayin al’ummar da suke jagoanta a zukatansu.


Ba zai zama alheri ba – ’Yan kasuwa

A nasu bangaren, ’yan kasuwar sun ce sake rufe garin zai jefa jihar cikin karin halin-ha-ula’in da yanzu suke ciki.

Faisal Idris Abdullahi wani matashin dan kasuwa a babbar kasuwar Shaik Abubakar Gummi da ke Kaduna, ya ce sake kulle jihar ba zai zama maslaha ba saboda a cewarsa, gwamnati ba ta da abun da za ta ba su.

“Ko fa kwanaki kafin Sallah sai da aka jibge jami’an tsaro a kusa da kasuwanninmu don kada ma mutane su ce za su shiga kasuwar; hakan sai yake nuna mana ko akwai laifin da ‘yan kasuwar suka yi wa gwamnatin ne

“Idan ka duba Kaduna ma ba ta cikin jihohin da suka fi fama da cutar nan amma ba a takura musu kamar yadda aka takura mana ba.

Faisal ya kuma shawarci gwamnan da ya mayar da hankalinsa wurin wayar da kan mutane amma ba sake kulle gari ba, yana mai cewa matakin ba zai haifar wa jihar da mai ido ba.