Shugaban Shabbabul kadiriya na Jihar Sakkwato Malam Ahmad Abdullahi Sa’i ya nemi fitaccen malamin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya janye kalaman da ya yi kan Mujaddadi Shehu Usman dan Fodiyo domin samar da zaman lafiya mai dorewa a Najeriya.
Shugaban wanda ya yi magana da manema labarai ne a madadin mabiya darikar kadiriyya a shekaranjiya Laraba, ya ce “darikar kadiriya da Tijjaniya a kasar nan kowa ya san irin fahimtar juna da suke da ita, domin dukkansu suna da fahimta daya wato kare waliyai, amma sai ga malamin da muke girmamawa ya zo ya yi kalaman batanci ga Shehu dan Fodiyo wadanda ba su yi dadi ga mabiya kadiriya ba.”
Shugaban ya ce “Ba mu da madogara ko sautin da za mu yi amfani da shi domin Sheikh dahiru ya fahimci mun yi masa adalci in ba mu fito ta kafafen watsa labarai mun yi kira gare shi da ya janye kalaman da ya yi tare da ba mu hakuri ba, ko kuma mu mayar masa da martani marar dadi, kan wannan muke son ya nuna kuskurensa don mu ci gaba da tafiya tare kamar yadda ake.”
Ya ce “A gaskiya Sheikh dahiru Bauchi ya ci wa Mujaddadi zarafi kuma abin mamaki shi dan Najeriya ne ya san ayyukkan da dan Fodiyo ya aiwatar a Najeriya da Afirka ta Yamma gaba daya, amma ya rufe idonsa domin yana bukatar ya fadi son ransa wanda ba za mu kyale ba dole mu yi magana.”
A karshe ya yi kira ga matasan kadiriya kada su yi kowace irin hatsaniya da za ta kawar da zaman lafiyar jihar, su bar lamarin a hannunsu da yardar Allah Sheikh dahiru Bauchi zai janye kalamansa da zarar ya ga wadanan kalamai nasu.
’Yan kadiriya sun nemi Sheikh dahiru Bauchi ya janye kalaman da ya yi kan Shehu dan Fodiyo
Shugaban Shabbabul kadiriya na Jihar Sakkwato Malam Ahmad Abdullahi Sa’i ya nemi fitaccen malamin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya janye kalaman da ya yi…