kungiyar ’yan jarida ta kasa reshen Jihar Gombe, ta yi Allah-wadai da wani DPO mai suna Williams Kashere saboda yadda ya doki dan jaridar gidan talabijin na kasa (NTA) har ya fasa masa kyamara.
Shugaban kungiyar ’yan jarida a Gombe, Alhassan Yaya, ya yi wannan koken ne a lokacin da yake bayyana wa ’yan jarida irin matsayin da kungiyar ta dauka na cewa ba za ta sake daukar duk wani labarin da ya shafi ’yan sanda a jihar ba kowanne iri ne.
Wannan mataki ya biyo bayan zaman da shugabanin kungiyar na NUJ suka yi ne a ranar Litinin din da ta gabata, don shaidawa duniya cewa daga wannan rana sun daina daukar duk wani labari da ya shafi ’yan sanda a jihar har sai baba ta gani.
Shugaban yace a ranar Alhamis din da ta gabata ce wani jami’in dan sanda mai mukamin DSP, wanda kuma DPO ne mai kula da wutar kan hanya, Williams Kashere da kansa ya daki ma’aikatan gidan talabijin na NTA, ya fasa masu kyamara, ya kuma sa aka watsa musu hayaki mai sa hawaye saboda sun yi aikinsu a kan ’yan sandan.
Ya yi kira ga Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mista Austin Iwar da cewa ya gaggauta gudanar da bincike a kan lamarin, sannan kuma a dauki matakin da ya dace a kan shi DSP Williams Kashere kuma su biya hukumar gidan talabijin na NTA kyamararsu da aka lalata da wayar ma’aikacinsu da ta bata a lokacin da suke dukansa.
Gaza yin hakan cikin gaggawa, shi ne zai sa duk wani aikin da ya shafi ’yan sanda babu wani dan jarida da zai sake zuwa don daukar rahoto. Sannan kuma NUJ ita ma tana da dama na daukar duk matakin da ya dace.
Shugaban na NUJ ya kara da cewa wakilan NTA suna tafiya ne sai suka ga wani abokin aikinsu ’yan sanda sun kama shi da babur wai ya karya dokar wutar kan hanya, ya ce su kai shi gida ya dauko katin shaidarsa da ya manta, ko idan ya nuna musu za su kyale shi. Shi ne ya gaya musu irin cuwa-cuwar da ’yan sandan suke yi, su kuma suka dana kyamara za su fara aiki sai DPO da kansa ya dinga dukansu.
Wakilan NTA din da aka yi wa duka su ne Lukman Abubakar da Shafa’atu Abdulmuminu, wacce ita har targade ta samu a hannu.