Ya zuwa yanzu kimanin ‘yan jarida goma da ke aiki a ofishin gwamnan jihar Akwa-Ibom ne ake zargi suna dauke da cutar coronavirus.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da fadar gwamnatin jihar ta qaryata rahoton da ke cewa mutum tara cikin mukarraban gwamnatin na dauke da cutar.
Makwanni biyu da karyata hakan sai wasu rahotanni ke nuni da cewa an samu mutum goma ‘yan jarida dake aikin daukar labarai a ofishin gwamnan anyi musu gwajin cutar coronavirus an kuma same su da ita,lamarin da ya jefa kungiyar ‘Yan jarida da al’ummar gari cikin firgici.
Idan za’a iya tunawa cutar ta lakume wani likita a jahar da ke aikin kula da wadanda coronavirus ta kama.
Wani dan jarida mai suna Etorobong Inyang na jaridar Edge News ya aike da sako a shafinsa na Facebook cewa an gayyaceshi asibitin kwararru na Ibom domin a tabbatar masa ya kamu da cutar coronavirus.
A nata bangare Uwargida Idongisit Ashemere shugabar kungiyar wakilan kafafen yada labaru cewa tayi “Nima an kira ni ta wayatar salula an bukace ni da in miqa kaina asibitin qwararru na Ibom aka tabbatar min cewa mutum goma ‘Yan jarida sun kamu da cutar kurona” inji ta.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa reshen jihar Akwa Ibom ba ta ce uffan ba.