✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan IPOB sun kashe ’yan Arewa 8 a Imo

An kashe su ne hare-hare tsakanin Juma'a zuwa Talata.

Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan Awaren Biyafara na IPOB ne sun hallaka mutum takwas, ’yan Arewacin Najeriya a wasu hare-hare da suka kai a sassan daban-daban na Jihar Imo.

Rahotanni sun ce biyu daga cikin mutanen da aka hallaka matafiya ne da ake kyautata zato an tura su aiki ne zuwa daya daga cikin Jihohin Kudu maso Gabas.

An aki hare-haren ne tsakanin daren Juma’a da ranar Talata.

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa a tsakanin kwanakin, maharan sun kashe ’yan Arewa mutum takwas a mabanbantan wurare da ke Jihar.

A cewarsa, “A garin Umuagwu, Karamar Hukumar Ehiama Mbono, ’yan IPOB sun kashe mutum biyu da daren Juma’a.

“Ko a daren Talata ma an samu karin kisan wasu da aka yi wa kwanton bauna aka kashe wasu mutum uku a kauyen Ayara, da ke Karamar Hukumar Mbono,” inji shi.

Bugu da kari, majiyar ta tabbatar da karin kisan wasu ’yan Arewa da ake zato an turo su aiki ne daya daga cikin Jihohin Kudu maso Gabas, suka tare mota suka fitar da su a Marabar Banana, Karamar Hukumar Urlu, su ma suka kashe su, jimlar mutum takwas kenan a dare biyu aka kashe.

Ya kuma ce sun kara kashe wasu mutum uku da ke yawon talla a kauyen Achangale, shi kuma yankin Karamar Hukumar Obowo, da ke Jihar.

“’Yan Arewa mazauna Jihar na ci gaba da nuna takaicinsu tare da bakin cikin yadda mahukuntan Jihar ke kawar da kai ba tare da daukar matakin hana wannan kisan na ’yan Arewa ba.

Wakilin mu ya tuntubi Rundunar ’Yan Sandan Jihar domin jin ta bakin su kakakinta, Mike Abattam, ya ce, “Ba mu samu rahoton faruwar hakan ba, amma da zarar mun samu za mu sanar da kai.”