Wasu ’yan ina-da-kisa sun kai hari tare da hallaka shugaban Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO), Farfesa Godswill Obioma a Minna babban birnin jihar Neja.
Matar mamacin, Misis Elizabeth Obioma ce ta tabbatar da hakan yayin zantawarta da ’yan jarida da safiyar ranar Talata.
- ’Yan sanda sun cafke ’yan kungiyar IPOB da makamai
- Gwamnatin Kano ta haramta shan sigari a bainar jama’a
“Ina kyautata zaton ’yan ina-da-kisa ne, sun zo sun hallaka shi ba tare da daukar komai daga gidan ba,” inji ta.
A cewarta, mijin nata bai jima da dawowa Minna ba daga Babban Birnin Tarayya Abuja lokacin da maharan da ke dauke da muggan makamai suka yi wa gidan nasa kwanton bauna tare da hallaka shi.
A baya dai marigayin ya yi ta fuskantar barazanar cire shi daga mukamin shugabancin hukumar ta NECO.
Mai kimanin shekaru 67 a duniya, Farfesa Obioma ya fara shugabancin hukumar ne a watan Mayun 2020.
Ya fito ne daga jihar Abiya da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
To sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na jihar ta Neja bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba domin jin ta bakin rundunar kan lamarin ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.