Ministar Jinkai, Agajin Gaggawa da Walwalar Jama’a ta kasa, Sadiya Umar-Farouk ta ce yanzu haka Najeriya na da ‘yan gudun hijira miliyan biyu.
Ministar ta bayyana hakan ne yayin da take amsa tambayoyin ‘yan jarida a Abuja ranar Alhamis game da ‘yan gudun hijira.
- ’Yan gudun hijira sun samu tallafin $50,000 daga Qatar
- ’Yan gudun hijira 800,000 ne a sansanoni ke bukatar tallafin abinci – Zulum
- Zulum ya ziyarci Chadi kan dawo da ’yan gudun hijira
- Boko Haram ta bindige ’yan gudun hijirar Najeriya 50 a Nijar
Sadiya ta ce, “Yanzu a Najeriya muna da ‘yan gudun hijira akalla miliyan biyu, wadanda matsalar ta’addanci ta ritsa da su.
“Aikin ma’aikatar nan shi ne samar da tallafi, da hanyoyin kyautata rayuwar wanda rikicin ta’addanci ya shafe su.
“Ma’aikatar nan na kokarin ganin an tallafi ‘yan gudun hijirar, wajen dawo da su muhalallansu, wasu kuma a gina musu gidajensu da suka rasa,” inji ministar.
Sadiya, ta kuma kara da cewa APC ita ce jam’iyya ta farko da ta taimaki masu bukata ta musamman, tun daga matakin mazabu har zuwa matakin tarayya.
A cewar Sadiya, shugaba Buhari na da shirin bada mukami daga cikin masu bukata ta musamman a cikin gwamnatinsa.
Idan ba a manta ba, a baya shugaban ya nada mai ba shi shawara na musamman a kan masu bukata ta musamman.