Kimanin ’yan gudun hijira 11 ne suka kone sannan wasu gommai suka sami munanan raunuka sakamakon tashin gobara a sansanin ’yan gudun hijira a garin Rann da ke Kala-Balge a jihar Borno a jiya.
Jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA da ma’aikatan lafiya sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 da minti 27 na dare ta kai har zuwa kimanin karfe uku na dare a sansanin ’yan gudun hijirar da ke garin Rann a karamar hukumar Kala-Balge.
Sun ce kananan yara da mata ne gobarar ta fi shafa.
Wani likita wanda yake aiki da wata kungiyar bayar da agaji ya fadawa Aminiya cewa “Mun kirga kimanin ’yan gudun hijira 11 wadanda suka mutu. Da yawa sun samu mummunar kuna kuma suna cikin mawuyacin hali. Muna iya kokarinmu mu ceto ransu”.
Ya bayyana cewa sakamakon karancin ruwa a sansanin ’yan gudun hijirar ba a kashe gobarar cikin lokaci ba “Muna fuskantar kalubale sosai”.
Kwadinetan hukumar agaji ta NEMA na yankin Arewa maso gabas, Bashir Idirs Garga ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya bayyana cewa mutum biyar ne suka mutu