A yayin da shirye-shirye suka yi nisa na gudanar da Babban Raron Jam’iyyar APC, Aminiya ta gano wasu mutane da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke son a ba su mukamai a Majalisar Gudanarwar Jam’iyyar.
Aminiya ta gano cewa gwamnoni da wasu manyan ’yan jam’iyar na kai gwauro suna kai mari don ganin ’yan gaban goshin Buharin su biyar ba su kai labari ba a taron na ranar Asabar.
- Farashin danyen mai ya kara tashi a kasuwannin duniya
- Kotu ta umarci a biya Sowere diyyar kamensa kan zanga-zangar juyin juya hali
Hakan ya haifar da rabuwar kai a tsakanin manyan ’yan jam’iyyar, inda masu goyon mutanen da Buhari ya zaba ke kokarin ganin duk yadda za a yi shafuffun da man sun sha.
Aminiya ta jiyo daga wata majiya mai karfi cewa, a wata wasika da Shugaba Buhari ya aike wa Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu, a ranar 18 ga watan Maris, Buhari ya yi kira da a kwantar da hankali a jam’iyyar, bayan dambarwar shugabanci tsakanin Buni da Bello.
A cikin wasiyar ya mika sunayen wasu mutum biyar da yake so a wasu mukamai da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar ta Kasa.
Mutanen su ne Sanata Abdullahi Adamu (Nasarawa, Shugaban Jam’iyya) da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ken Nnamani (Enugu, Mataimakin Shugaban Jam’iyya daga Yankin Kudu).
Sauran su ne Injiniya Ife Oluwa Oyedele (Ondo, Sakataren Jam’iyya); Honorabul Farouk Adamu Aliyu (Jigawa, Saktaren Tsare-tsare) da kuma Arc Waziri Bulama (Borno, Mataimakin Shugaban Jam’iyya daga Arewa).
‘Makircin’ CPC
Aminiya ta gano daga majiyoyinta a APC cewa mukarraban Buhari da suka ziyarce shi lokacin da ya je London ganin likita, wato Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, suna dsa hannu a wasikar da Buharin ya aike wa Bagudu.
Majiyoyin daban-daban sun tabbatar wa wakilinmu cewa ministocin biyu da wasu makusantan Buhari sun gamsar da shi game da bukatar ya bayyana ra’ayinsa kan al’amuran jam’iyya ta hanyar bayyana mutanen da yake so a wasu muhimman mukamai, kafin karewar wa’adin mulkinsa.
“Sun mika mishi sunayen mutanen da suka gamsu da su a wasu mukamai, yawancinsu kuma daga tsohuwar jam’iyyar CPC.
“Buhari ya amince da jerin sunayen, ya kuma hada shi da wasikar da Buhari ya aika wa Bagudu,” inji wata majiya a Fadar Shugaban Kasa.
“Sun bayyana wa Shugaban Kasa cewa idan ya bari gwamnoni suka samu yadda suke so, to mutanensa babu abin da su samu, wanda hakan zai kawo karshen tasirin Buhari ko magadansa a siyasa,” inji wani babban jigo a jam’iyyar APC.
In banda Sanata Adamu da Sanata Nnamani da suka fito daga bangaren jam’iyyar PDP da suka dawo APC, sauran mutum ukun dadaddun na hannun daman Buhari ne.
Honorabul Farouq Aliyu, wanda tsohon dan Majalisar Wakilai ne baban kusa ne a tsohuwar jam’iyyar CPC, wadda a karkasin inuwarta ya yi takarar Gwamnan Jihar Jigawa a 2011.
Shi kuma Injiniya Oyedele, wanda shi ne Babban Darakta a Hukuma Wutar Lantarki ta Neja Delta (NDPHC), mamba ne a Kwamitin Amintattun tsohuwar jam’iyyar CPC.
Arc Bulama kuma, tsohon mamban Kwamitin Zartarwar (NEC) tsohuwar jam’iyyar CPC ne kuma ya taba zama Sakataren Jam’iyyar APC na ksa na dan lokaci kafin a rushe shugabancin a kafa kwamitin rikon jam’iyyar na yanzu.
Yunkurin dasa manyan kusoshin CPC a Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar ya yi karfi ne bayan zabo Sanata Abdullahi Adamu ya zama Shugaban Jam’iyyar na Kasa.
Wata majiya mai karfi ta ambato wani minista daga yankin Kudu da ke neman takarar shugaban kasa, ya ce bangaren CPC sun yi saurin daukar matakin ne bayan ganin Buhari ya zabo Sanata Abdullahi Adamu, inda suke ganin akwai yiwuwar su koma ’yan kallo.