✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ga-ruwa sun shiga yajin aiki a Kano

Ana zargin dan ga-ruwan ya rasa idonsa guda daya sakamakon rauni da aka yi masa.

Karancin ruwa ya mamaye unguwar Hotoron Danmarke da kewaye sakamakon yajin aiki da zanga-zanga da masu ga-ruwa suka yi.

Binciken Aminiya ya gano ’yan ga-ruwan sun shiga yajin aiki ne bayan wasu ’yan unguwar sun lakada wa wani dan garuwa duka, har suka fasa masa ido, saboda ya ki sayar musu da ruwa.

Wani dan ga-ruwa mai suna Malam Yahuza Lawan, wanda ganau ne, ya ce yanzu abokin sana’ar tasu, “Yana asibiti yanzu haka ana duba lafiyarsa, amma likitoci sun sanar da mu cewa ya rasa idonsa guda daya sakamakon tsananin duka da ya sha.

“Dole ne mu yi zanga-zanga kan abin da aka yi wa dan uwanmu; Mutane sun dade suna cin zarafinmu, ba zamu ci gaba da hakuri ba,” cewar Lawan.

Ya ce mutanen da ake zargi sun tare mai sayar da ruwan da ya makare kurar ruwansa don ya sayar musu ta karfin tsiya, alhali ya riga ya yi wa wasu alkawari zai kai musu ruwan.

Da dan ga-ruwan ya ki sayar wa mutanen da suka tare shin, sai suka hau shi da duka, suka yi masa rauni da ya yi sanadin rasa idonsa daya.

Wani mai gidan ruwa a unguwar, Adamu Khalil, ya ce shi ma ya rufe gidan sayar da ruwansa saboda mara wa abokin kasuwancinsa baya.

“Sun yi masa dukan kawo wuka saboda kawai ya ki sayar musu da ruwa, bayan tun da farko ya ce su bari ya kai wa wani mutum da ya biya kudinsa kafin ya dawo ya kawo musu.

“Mun dakatar da komai har sai an dauki matakin da ya dace.

“Mun samu labarin ’yan sandan caji ofis na Hotoro sun cafke wanda ake zargi da aikata laifin don haka muna bukatar a yi masa adalci,” in ji Khalil.

Binciken da Aminiya ta yi ya gano zanga-zangar ta haddasa karancin ruwa a ranar Alhamis a unguwanin Hotoro Danmarke, Hotoro Bayan Defo, Unguwa Uku, Kauyen Alu da sauransu.

Bayan tuntubar kakakin ’yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce zai gudanar da bincike kan lamarin.