✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashin jirgin ruwa sun sace mutum 8 a Bayelsa

An sace su ne a kan hanyarsu ta dawowa daga jana’iza

Wasu ’yan fashin jirgin ruwa sun sace fasinjoji takwas da suka dawo daga bikin binne gawa a kan wani jirgin ruwa daga Brass zuwa Yenagoa a Jihar a Bayelsa.

Jirgin dai na dauke da fasinjoji 15 a kansa lokacin da ya bar Egweama a Karamar Hukumar Brass da ke Jihar.

Fasinjojin dai na kan hanyarsu ce ta dawowa daga bikin binne gawa a karshen mako, inda ’yan ta’addan suka yi musu kwanton bauna a tsakiyar teku.

Wata majiya daga yankin ta ce an kwashe mutanen ne sannan aka yi gabar tekun da su, yayin da ragowar mutum bakwai kuma suka tsere.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, masu garkuwar ba su tuntubi iyalan mutanen ba don neman kudin fansa.

Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jiragen Ruwa ta Karamar Hukumar Brass, Daniel Bioduomoye ya tabbatar da faruwar harin.

Ya ce, “’Yan fashin sun tare jirgin mai karfin inji 200 kusa da wata gonar shinkafa, sannan suka yi awon gaba da takwas daga cikin su 15.”

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da harin ya ce yanzu haka suna nan suna gudanar da bincike don kamo barayin.