✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan fashi sun kashe dan sanda a Kuros Ribas

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kuros Ribas, Hafiz Inuwa Mohammed, ya tabbatar da kisan da aka yi wa jami’in dan sanda Ebri Ogban wanda ‘yan fashi…

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kuros Ribas, Hafiz Inuwa Mohammed, ya tabbatar da kisan da aka yi wa jami’in dan sanda Ebri Ogban wanda ‘yan fashi da makami suka yi masa.

A yayin da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar ‘yan sanda (PPRO) Misis Irene Igbo ke jawabi ta ce, Inuwa ya sanar da cewa lokacin da jami’an ‘yan sandan suke bakin aiki a ofishinsu sai suka samu rahoton cewa, ‘yan fashi da makamai sun tare hanyar Otop Abasi dake cikin Kalaba babban birnin jihar.