Wasu ’yan fashi sun kai wa mai tsaron baya na Manchester City, Joao Cancelo hari, lamarin da ya jikkatar da dan wasan mai shekara 27.
Cikin wani hoton bidiyo da dan wasan ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya yadda ’yan fashin suka ji masa rauni a fuska sakamakon turjiya da ya yi yayin kai masa harin.
- Nawa kake bukata ka iya rike aure?
- Mai tsananin rabo ne kawai zai iya ganin karshen mulkin Buhari a raye – PDP
“Wasu matsorata hudu sun cutar da ni kuma sun yi kokarin cutar da iyalina, wanda a dalilin haka na yi rikici da su har ta kai ga sun ji min ciwo.”
Bayanai sun ce ’yan fashin sun kwace sarkokinsa na zinare da na iyalinsa amma basu cutar da iyalin nasa ba face raunin da suka ji masa a fuska.
Cancelo ya ce faruwar wannan lamari ba zai karya masa gwiwa ba wajen bayar da gudunmawar da ta kamata a wasan Firimiyar Ingila da kungiyarsa za ta yi da Arsenal a yau Asabar.
A watan Agustan 2019 ne Manchester City ta sayo Cancelo daga Juventus, inda a yanzu yana cikin ’yan wasan da ke taka rawar gani a cikin tawagar ta Pep Guardiola wadda ke zaman ta daya teburin Firimiyar da tazarar maki 8 tsakaninta da mai biye mata Chelsea.
Tuni dai Manchester City ta fitar da sanarwar da ke tir da farmakin kan mai tsaron bayan nata tare da nuna goyon baya gareshi.
A sanarwar, Manchester City ta ce ’yan fashin sun kai wa dan wasan farmaki ne a gidansa da ke Arewacin Landan a ranar Alhamis.