Rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa, ta sanar cewa wasu da ake zargi ’yan fashi da makami ne sun harbe wani hafsan sojan kasa, Manjo M.S Isma’il sannan sun raunata wani Pte. Harisu Aliyu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Lawan Shittu ya tabbatar da faruwar hakan yayin ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ranar Talata a birnin Dutse.
- Buhari ya umarci a gaggauta ceto duk daliban da aka sace
- Firimiyar Najeriya: Nasarawa United ta tunkudo Pillars daga mataki na biyu
A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuli a kan babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri.
ASP Shittu ya ce ’yan fashi da makamin sun kai wa sojin biyu hari yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna bayan tasowa daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
“Da misalin karfe 9 na daren ranar 4 ga watan Yuli, ofishin ’yan sanda na Fanisau ya samu rahoton cewa ’yan fashi da makami sun datse babbar hanyar Maiduguri daidai Kauyen Dindibis a Karamar Hukumar Dutse.
“Tawagar ’yan sandan mu ta sintiri ta isa wuri da ke da tazarar mita 40 tsakaninsa da Kauyen Dindibis, sai dai kafin zuwansu ’yan fashin sun tsere cikin jeji.
“Karamin sojan, Pte. Aliyu ya samu rauni a wuyansa, yayin da suka harbe Manjo Isma’il kuma ya mutu nan take,” a cewarsa.