Wasu ’yan fashi sun fille kan mai gadin gidan dan majalisar dokokin Jihar Imo, Ekene Nnodumele, a ranar Laraba.
Bayan fille wa mai gadin kai, maharan sun kuma cinna wuta a gidan dan majalisar da ke Ebenator, Awo Omama a Karamar Hukumar Orsu ta Jihar.
Wakilinmu ya rawaito ’yan fashin sun kuma kona gidan tsohon Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’ar Jihar, Cyprain Charles Akaolisa a yankin.
Ndumele ya bayyana kaduwarsa kan yadda maharan suka kai harin suka fille kan mai gadin gidan nasa a yayin farmakin.
Ya ce “Ban taba tsammanin hakan ba saboda ni ba mafadaci ba ne, ba na takun saka da kowa.
“Ina wakiltar mutanen yankin Orsu yadda ya kamata. Mutanenmu ba masu tashin hankali ba ne. Ina da tabbacin turo su aka yi. Kashe mutane ba dabi’ar mutanen Orsu ba ce.”
Ndumele ya bayyana kisan gillar da aka yi wa mai gadin gidansa a matsayin rashin imani.
“Ba na tunanin akwai mutumin da ya kamata a ce ya mutu a haka. Ba wai kashe shi kadai suka yi ba, fille masa kai suka yi. Ban taba cin zarafin wani ba ko musguna wa mutanen Orsu,” a cewarsa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar, SP Bala Elkana, ya ce jami’an ’yan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin.
A cewarsa, “Mun baza kwararrun jami’ai a yankin, ana ci gaba da bincike a yanzu. Nan gaba za mu bayar da cikakken bayani.”