Wasu mutum biyu da ke zargi da laifin fashi da makami a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo sun yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar duro wa daga wani ginin bene mai hawa biyu a kotun da ke sauraron tuhumar da ake yi masu.
Mai gabatar da ƙara a Kotun Majastare ta Iyaganku da ke Ibadan, Sufeton ‘yan sanda Femi Omilana ya ce, tun cikin shekarar 2023 kotu ta bayar da umarnin tsare waɗanda ake zargin.
- Sojin sama sun kashe ’yan bindiga 30 a Katsina da Borno — NAF
- Muhimman dokoki 10 a shekaru 25 na Dimokuraɗiyyar Najeriya
Ya bayyana ana tuhumar waɗannan mutane — Damilare Adeniran da abokinsa Victor — tare da wasu uku da laifin yin amfani da bindigogi da wasu makamai wajen yi wa jama’a fashi.
Ya ce, waɗannan ‘yan fashi sun kuɓuce daga hannun jami’an tsaro a cikin Kotun ne suka yi kasadar tsallaka tagar Kotun da suka duro ƙasa inda suka samu munanan raunuka a sassan jikinsu.
Sufeto Omilana ya ce ‘yan fashin sun duro ƙasa ne a daidai lokacin da Alkali G. Oladele na Kotun Majastare yake sauraron ƙarar da ake tuhumarsu a ranar Laraba.
Ya ce an garzaya da su zuwa Asibitin don kula da lafiyarsu inda za a ci gaba da tsare su a gidajen yari.
Alƙalin Kotun ya ɗage ci gaba da sauraron tuhumar da ake yi musu zuwa ranar 8 ga watan Yuli mai zuwa.