’Yan sanda sun cafke gungun wasu ’yan fashi da makami da suka kware wajen amfani da tsafi su fasa gidaje a Karamar Hukumar Daura ta Jihar Katsina.
Kakakin ’yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya ce ’yan fashin da dubunsu ta cika sun hada da wani mai shekara 50 da mai shekara 25 – daga Jigar Jigawa; na ukunsu kuma shekarunsa 23 kuma ya fito ne daga Kano.
- NAJERIYA A YAU: Zaben 2023: Shin Yakin Neman Zabe A Kafafen Sada Zumunta Zai Yi Tasiri?
- Karyewar gada ya jawo asarar rai a Zariya
Ya ce, dubun bata-garin ta cika ne bayan ’yan sanda sun samu bayanan sirri inda “Muka dakile su tare da cafke bayan sun kutsa cikin wasu gidaje biyar a Daura, sun yi awon gaba da kayan masu gidajen.
“Wadanda ake zargin sun shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa sun yi amfani da layoyoyi ne sun sa masu gidaje barci har sai sun gama aikata barnar tasu.”
SP Gambo Isah ya ce, sun kuma amsa cewa sun samo layoyin ne daga wani boka a Jamhuriyar Nijar.
Ya kara da cewa abubuwan da aka kwato daga wajensu sun hada da makullan da aka kirkira, kayan balla kofa; adduna; layukan waya guda biyar da kuma layoyi da sauransu.
Ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bayan sun kammala bincike.