✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daban daji sun kashe mutum 11 a Katsina

Mutane ukun da suka jikkata na kwance a babban Asibitin Dutsin-Ma inda suke samun kulawa.

Akalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon wani sabon hari da ’yan daban daji suka kai kauyen Tsatskiya da ke Karamar Hukumar Safanan Jihar Katsina a ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa, yanzu haka mutane ukun da suka jikkata na kwance a babban Asibitin Dutsin-Ma inda suke samun kulawa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 9.30 kuma ana kyautata zaton daukar fansar wani mai yi musu liken asiri da aka kashe ce ta sanya suka kawo harin.

Aminiya ta ruwaito cewa, kwanaki hudu kafin aukuwar lamarin, mazauna kauyen Hakon Kartakawa sun samu nasarar zakulo wani mai yi wa ’yan bindiga leken asiri daga cikinsu kuma suka dauki hukunci a hannunsu.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, maharan da suka kai farmakin haye a kan Babura nan take sua fara harbi kan mai uwa da wabi wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 11.

Makamancin wannan hari da ’yan bindiga ke kai wa wata hanya ce ta aiken sakon gargadi ga mazauna a kan kashe duk wanda ke samar musu da bayanai.

A halin yanzu, mazauna kauyuka na ci gaba da tserewa suna barin mahallansu zuwa garin Dutsin-Ma domin neman mafaka ta tsaron lafiyarsu.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa wanda ya inganta rahoton yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Dikko, ya ce mutum uku kacal aka kashe sabanin 11 da mazauna kauyen ke ikirari.