✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun kashe ’yan sanda 2 da wasu 28

’Yan daba sun kashe mutum 30 ciki har da ’yan sanda biyu a wani rikici a Port-au-Prince, babban birnin kasar Haiti.

’Yan daba sun kashe mutum 30 tare da jikkata wasu da dama a wani rikici a Port-au-Prince, babban birnin ƙasar Haiti.

’Yan sanda biyu na cikin mutanen da aka kashe, baya ga gidaje da dama da aka ƙoƙƙona a rikicin na ’yan daba a unguwar Carrefour-Feuilles da ke birnin.

Wata ’yar ungwuar, Dominique Charles, ta ce ’yan daba sun kashe ɗanta da ’yan uwanta uku da mahaifiyarta da kuma mijin mahaifyar ta hanyar jefa “bom ɗin kwalba a cikin gidanmu ya kashe kowa, ni kaɗai na tsira.”

Jami’an lafiya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce yawan mutanen da aka kashe na iya ƙaruwa kuma iyalai na ƙaurace wa  gidajensu a yankin saboda fargabar dawowar rikicin.

Hukumomi sun ce rikicin kwanan nan ya raba mutum sama da 5,000 da gidjensu, suka koma fakewa a makarantu da wata cibiyar wasanni da kuma kan tituna.

A ranar Alhamis gwamnati ta fara rabon abinci ga mutane da rikicin ya shafa a ƙasar ta Haiti mai fama da matsalolin tsaro da na siyasa da kuma matsin rayuwa, ga kuma gwamnati da hukumomin tsaro masu rauni.

Carrefour-Feuilles unguwa ce da ta yi ƙaurin suna wajen ayyukan ’yan daba kusan kulla-yaumin a birnin Port-au-Prince.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa bata-gari ke iko a kusan kashi 80 din yankin inda suke yin ƙwacen motoci, fyaɗe, fashi da kuma garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.