✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole a kama masu sukan Kwankwaso —Naburaska

Jarumin barkwanci na Kannywood, Mustapha Naburaska ya yi kira ga Hukumar Tace finafinai ta Kano ta kama masu cin mutuncin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Fitaccen jarumin barkwanci na Kannywood, Mustapha Naburaska ya yi kira ga Hukumar Tace finafina ta Jihar Kano da ta fara kama masu cin mutuncin jagoransu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A wani bidiyo da ya wallafa a Instagram, jarumin wanda tsohon SA Farfaganda ne ga tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya ce idan hukumar ta kasa kama su to ta gaza a aikinta.