✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daba sun kashe mutum uku a zanga-zangar #EndSARS

'Yan daba da suka shiga zanga-zangar #EndSARS sun yi kisan gilla a Ketu, Jihar Legas

Zanga-zangar #EndSARS ta kazance inda ’yan daba dauke da muggan makamai suka rika kai wa ’yan tireda da sauran jama’a hari da safiyar Talata.

‘Rahotanni sun ce ’yan dabar sun kashe akalla mutun uku tare da jikkata wasu da dama a kan hanyar Ketu-Ojota da ke Jihar Legas.

Shaidu sun ce maharan sun jefa jama’a cikin zaman dar-dar a yayin da ake ci gaba da zanga-zangar ta #EndSARS, wadda tun ranar Asabar ta fara kazancewa a jihar bayan ’yan daba sun shiga ciki.

Masu zanga-zangar sun tare hanyar Ikorodu a daidai tashar mota da ke Ketu suna wake-waken #EndSARS da kuma kin jinin mummunan shugabanci.

Farmakin da ’yan daban suka kai ya tilasta wa ’yan kasuwa da fasinjoji da ke jiran ababen hawa ranta a na kare domin neman tsira.

Rahotanni sun nuna kungiyoyin asiri sun  kwace ragamar zanga-zangar da nufin daukar fansa a tsakaninsu.

Bayanan da muka samu sun nuna an kashe mutum ukun ne a rikicin kungiyar ‘yan kasuwa da ta ‘yan asiri a yankin.

Wani shaida ya tabbatar wa wakilinmu cewa ‘yan kungiyar asirin sun cire kokon kan daya daga cikin mutanen da suka kashe sannan suka yi ta yawo da ita bayan sun kafa ta a kan ice.

“Yanzu haka ana cikin fargaba a yankin Ketu da Kasuwar Mile 12 kuma ‘yan tireda sun rufe shagunansu domin tsoro”, inji shaidar.