✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daba sun kashe mutum, sun jikkata wasu a wurin zabe

An harbe mutum daya har lahira, wasu da dama kuma sun jikkata a lokacin da bata-garin suka yi dirar mikiya a wuraren zabe

Mutum daya ya rasu, wasu da dama sun samu raunuka bayan ’yan daba sun kai farmaki a rumufunan zabe a sassan Jihar Legas.

Aminiya ta gano cewa an harbe mutum daya har lahira, wasu da dama kuma sun jikkata a lokacin da bata-garin suka yi dirar mikiya a wuraren zaben.

Yankunan da aka kai hare-haren sun hada da Ikota, Jakande, Ijegun, Festac da kuma Isolo.

Rikicin ya fara barkewa ne bayan bata-garin sun kutsa cikin yankin Okota, inda jam’iyyar LP ke da karfi.

Maharan sun fatattaku mutanen da suka fito yin zabe, sannan suka lalata akwatunan zabe, suka tafi da wasu.