✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daba sun kai wa ’yan kwadago samame a Kaduna

’Yan sanda sun watsa mamayar da ’yan daba suka yi wa ofishin kungiyar kwadago

’Yan daba sun yi sammako wajen mamaye ofishin Kungiyar Kwadago ta Kasa, reshen Jihar Kaduna, inda ’yan kungiyar kwadago ke taruwa domin fara gudanar da zanga-zangar lumana a Kaduna.

Kimnan ’yan daba 100 ne ’yan kwadagon suka iske a ofishinsu dauke da makamai, lamarin da ya haddasa zullumi.

Daga baya kungiyar ta sanar da jami’an tsaro kuma ’yan sanda sun yi nasarar tarwatsa bata-garin har suka tsare mutum 20 daga cikinsu.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya tabbatar da lamarin, kuma ya ce an samar da jami’ai domi su yi wa tufkar hanci.

Tun a ranar Talata wasu ’yan daba suka kai farmaki ga ’yan kwadagon da ke zanga-zagar neman Gwamna El-Rufai ya dakatar da sallamar dubban ma’aikata da ya yi.

Sai dai ’yan kwadagon sun yi nasarar fatattakar ’yan daban da suka yi zargin hayar su aka dauka domin goga wa zanga-zangar kashin kaza.

%d bloggers like this: