✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daba sun jikkata mutum 17 a ayarin A.A Zaura

'Yan daban sun ji wa mutum 17 rauni sannan sun lalata motoci 17.

’Yan bangar siyasa sun kai hari kan ayarin yakin neman zaben dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, inda suka jikkata mutum 17.

Daraktan yakin zaben A.A Zaura, Yahaya Adamu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Gayawa a Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.

Takardar da ya aike wa kwamishinan ’yan sandan jihar da ’yan jarida ta ce, “Bincikenmu ya gano zuwa yanzu mutum 17 ne suka samu rauni sakamakon harin da aka kai mana.

“Wadanda suka ji rauni suna Asibitin Murtala ana kula da su, sannan motocinmu 17 duk an lalata su.”

Adamu ya bukaci kwamishinan ’yan sandan jihar ya gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace.

Idan ba a manta ba a baya-bayan nan, Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya gargadi ’yan siyasa da ake kokarin tada tarzoma a lokacin yakin neman zabi.

Kazalika, ya kuduri aniyar saka kafar wando daya da duk dan siyasar da aka samu da hannu wajen tayar da zaune tsaye a lokacin yakin neman zabe da ma lokacin zabe.