✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun cinna wa ofishin Sanata Barau Jibrin wuta a Kano

Rahotanni na cewa ’yan sanda sun mamaye gidan Malam Ibrahim Shekarau a safiyar Alhamis.

Rahotanni daga Jihar Kano sun ce ’yan daba sun kai hari tare da cinna wuta a ofishin yakin neman zaben  Sanata Barau Jibrin a matsayin gwamnan Kano

Hotunan da aka yada sun suna yadda ’yan dabar suka mamaye ofishin tare da yayyaga allunan fastoci da kuma tayar da yin kone-kone a ofishin da ke Titin Maiduguri a Kano.

Da yake tabbatar da harin, Sanata Barau, mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya ce, “Sun kona ofishin yakin neman zabena gaba daya, wace irin siyasa ce haka da har za a kona ofishin yakin neman zabe?”

Kawo yanzu babu dai tabbacin dalilin harin da aka kai ofishin yakin neman zaben na Sanata Barau, wanda bangarensa da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekaru suka sa zare da bangaren Gwamna Abdullahi kan shugabancin jam’iyyar APC a jihar.

Wasu rahotanni kuma sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a Gidan Sanata Shekarau a safiyar ta Alhamis.

Mun tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, game da lamarin amma ya ce suna kokarin shawo kan lamarin, don haka nan gaban zai nemi wakilinmu.

Amma kafafen yada labarai sun ruwaito Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ismaila Shuaibu Dikko yana cewa, “Abun ya koma hannunmu, jami’anmu sun kwace wurin suna bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.”

Wannan dambaruwa na zuwa ne washegarin wata takaddama kan rufe ofishin lauyan bangaren Sanata Shekarau da Sanata Barau, wato Mista Nureini Jimoh (SAN).

Lauyan shi ne ya kare bangaren Shekarau a shari’ar da suka kayar da bangaren Gwamna Ganduje a rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Jihar.

Sai dai sa’o’i kadan bayan jami’an gwamnatin Kano da ’yan sanda sun rufe ofishin lauyan aka sake bude shi.