✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun cinna wa caji ofis wuta a Ebonyi

Bata garin sun zargi 'yan sandan jihar da ba wa Fulani Makiyaya mafaka.

Wasu bata gari da ake zargin masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) ne sun kone ofishin ’yan sanda da ke yankin Isu a Karamar Hukumar Onitsha, Jihar Ebonyi.

Kakakin  Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Loveth Odah, ta maharan na daren Juma’a sun kuma kone motocin sintirin ’yan sanda hudu a cajis ofis din.

“Wannan ya faru ne bayan zargin da suke yi cewa ’yan sanda na ba wa Fulani makiyaya tsaro, wanda a sanadin haka daya daga cikinsu mai suna Nwite Njoku ya mutu.

“Dan sanda daya ya samu rauni a kafa sakamakon sara da adda da aka yi masa, amma yana murmurewa bayan ba shi kulawa a asibiti.”

Odah ta kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Aliyu Garba, ya je wajen tare da gane wa idonsa irin barnar da aka yi.

Ta ce Kwamishinan ya nemi zama da masu ruwa da tsaki a yankin don ganin an cafke wadanda suka aikata laifin.

“Kwamishina ya ba wa jama’a tabbacin ci gaba da tsare rayukansu da dukiyoyinsu, sannan ya bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa,” inji ta.