✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ci-rani 22 sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Madagascar

Sun nitse ne a kokarinsu na tsallakawa su shiga Faransa

Akalla ’yan ci-rani 22 ne suka mutu bayan jirgin ruwan da suke ciki ya nitse a kusa da wata gabar ruwa da ke kasar Madagascar a ranar Asabar.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasar (APMF) ce dai ta sanar da hakan a ranar Litinin a cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, “Mutum 47 sun yi lodin wuce ka’ida a kan jirgin, inda suka doshi garin Mayotte da ke kasar Faransa, amma jirginsu ya nitse.

“An sami nasarar ceto mutum 23 daga cikin fasinjojin, amma wasu 22 sun mutu.”

Hukumar ta kuma ce hatsarin ya auku ne ranar Asabar, kuma ana ci gaba da aikin ceto ragowar mutum biyun da har yanzu ba a ga gawarsu ba.

’Yan ci-rani da yawa ne duk shekara suke kokarin shiga Faransa ta garin, wanda ke kan iyakar Arewacin Madagascar da kuma tekun Indiya.

Ko a shekarar 2021 ma, sama da mutum 6,500 ne aka tsare yayin da suke kokarin tsallakawa ba bisa ka’ida ba, kamar yadda hukumomin Faransar suka tabbatar.

Babu dai cikakkun alkaluma a kan ainihin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a kokarinsu na tsallaka ruwan domin shiga nahiyar Turai musamman daga Afirka.

Wani rahoton Majalisar Dattawan Faransa da aka wallafa a shekarun 2000, ya yi kiyasin cewa akalla mutum 1,000 kan mutu a kowacce shekara.

(AFP)