Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta fara gano masu daukar nauyin ayyukan Boko Haram da ’yan bindiga da suka addabi sassan Najeriya.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ne, ya bayyana haka a cikin wata tattaunawarsa da gidan Talabijin na Channels, a ranar Talata.
- Rashawa: Mun kwato sama da N500m a Kano — Muhyi
- ’Yan bindiga sun kashe Limami da wasu uku a Binuwe
- Buhari zai yi kasafin sayen makamai da rigakafin COVI-19
- Zulum ya raba wa iyalai 100,000 tallafi a Monguno
“Jami’an tsaro suna aiki tukuru wajen ci gaba da bankado masu daukar nauyin Boko Haram.
“Yawanci ’yan canji ne ke tura kudaden da ake daukar nauyin ta’addanci a kasar nan, saboda akwai wanda aka cafke a Hadaddiyar Daular Larabawa, amma da zarar an kammala bincike mutane za su girgiza da sunayen da za su gani,” cewar Garba Shehu.
Ya kara da cewa an kuma gano cewa akwai manyan mutane daga ciki da wajen Najeriya da ke daukar nauyin tayar da hankulan mutane don biyan bukatun kansu.
Garba Shehu ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta raga wa duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin.
Alakar Boko Haram da ’yan bindiga
“Akwai kwararan hujojji da suka bayyana mana cewa akwai alaka tsakanin Boko Haram da wasu ’yan bindiga da suka addabi wasu yankunan Najeriya.
“A binciken, mun gano yadda Boko Haram ta aike wa wasu ’yan bindiga makamai, kuma wasu ne ke daukar nauyinsu,” a cewarsa.
Matsalar tsaro a Najeriya abu ne da ya dade yana ci wa gwamnatocin Najeriya tuwo a kwarya.
Lamarin da ya jawo salwantar rayuka, dukiyoyi da kuma koma baya ga tattalin arziki, musamman a yankin Arewa maso Gabas da Arewa ta Yammacin kasar.