✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Boko Haram ‘sun sake kwace’ garin Dikwa

“A yanzu haka, Boko Haram ce take iko da garin, suna ta yawonsu a garin."

Dubban mazauna garin Dikwa a Jihar Borno ne harin Boko Haram ya ritsa da su bayan mayakan sun yi wa garin kofar rago a daren ranar Litinin.

Majiyoyin Aminiya a garin sun a yanzu haka mayakan Boko Haram din ke da iko da garin suna sintiri ba tare da wani tsora ba ko fargaba.

Wani mazaunin garin, Bukar Ahmed ya shaida wa Aminiya cewa mayakan “Sun ce kada mu kuskura mu gudu, ba cutar da mu suka so yi ba, sojoji ne za su cutar da mu. Yanzu haka baburansu da motocin yakinsu na cikin garin.

“A yanzu haka Boko Haram ce ke iko da garin, suna ta yawonsu a garin. Ku taimaka ku rokar mana Shugaban Kasa ya ceci rayuwarmu,” inji shi cikin tashin hankali.

Mazauna sun ce tun ranar Litinin da maraice mayakan suka kwace garin kuma tuni suka kutsa kai cikin wani matsuguni mallakar Majalisar Dinkin Duniya.

Wani ma’aikacin jinkan ya ce, “Yanayin da muke ciki a Dikwa yanzu na da ban tsoro, dubban mutane ne yanzu aka ritsa a garin, muna bukatar agajin gaggawa domin tsira da rayuwarmu.

“Yanzu garin a hannunsu yake, dole gwamnati ta yi abin da ya kamata domin ceto mutane a kan lokaci.”

Tun da farko sojoji sun dakile yunkurin mayakan na kai hari garin, amma daga bisani suka sake dawowa bayan wasu ’yan sa’o’i.

Mazauna garin dai sun ce yanzu haka mayakan na Boko Haram na ta karakaina a bainar jama’a tare da gargadinsu da kada su kuskura su bar garin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ’yan ta’addan na kuma shaidawa jama’a cewa suna tare da su.

Garin Dikwa mai nisan kimanin kilomita 90 daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno ya jima yana fuskantar hare-haren kungiyar tun bayan da sojoji suka kwato shi a shekarar 2016.

Garin ne kuma kuma ke da sansanin soji na musamman inda sojojin da kugniyar ta tarwatsa sansaninsu a garin Marte kwanakin baya suka samu mafaka kafin daga bisani a kwato Marten daga mayakan da taimakon rundunar da ke Dikwa.

Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa Najeriya ya ziyarci sansanin na Dikwa a makon jiya, inda ya bayar da umarnin kwato Marte mai nisan kilomita 20 daga Dikwan daga hannun Boko Haram.

Wani mazaunin garin, Bukar Ahmed ya bayyana wa Aminiya halin da suke ciki a garin.

“Sun ce kada mu kuskura mu gudu, ba sun zo su cutar da mu ba ne, sojoji ne za su cutar da mu ba su ba. Akwai baburansu da motocin yaki yanzu haka a cikin garin.

“Maganar da nake da kai a yanzu haka, Boko Haram ce take iko da garin, suna ta yawonsu a garin. Ku taimaka ku rokar mana Shugaban Kasa ya ceci rayuwarmu,” inji shi, yayin da yake shasshekar kuka a waya.

Wani ma’aikacin jinkai ya ce ’yan ta’addan sun mamaye ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke garin.

Ya zuwa yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai yayin da sojoji ke ci gaba da fafutukar ganin sun kwato garin.

Ma’aikacin jinkan ya ce, “Yanayin da muke ciki a Dikwa yanzu yana da ban tsoro, dubban mazauna garin ne yanzu aka yi wa kofar rago, muna bukatar agajin gaggawa domin tsira da rayuwarmu.

“Yanzu garin a hannunsu yake, dole gwamnati ta yi abin da ya kamata domin ceto mutane a kan lokaci,” inji shi.