Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari kan ayarin motocin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, inda suka kashe dan sanda daya.
Rahotanni sun ce an kai wa ayarin Gwamna Buni hari ne a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Asabar, inda aka jikkata wasu ’yan sandan su biyu.
- Babu ɗalibin da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi a mulkina – Tinubu
- Isra’ila ta kai ƙazaman hare-hare makarantar Al Fakhoura a Arewacin Gaza
Gwamnan na kan hanyarsa ce ta komawa Damaturu bayan ya halarci taron yaye dalibai karo na 24 na Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno.
Wani ganau da ke cikin tawagar ya ce maharan sun bude wuta kan ayarin motocin ne daga bangarorin biyu na babbar hanyar, inda suka nufi direbobin motar.
Majiyar ta ce “Mun tsira da kyar a yau, an kai wa ayarin motocinmu hari ne a tsakanin garin Beneshiekh da Mainok mai tazarar kasa da kilomita 60 zuwa Damaturu bayan halartar taro karo na 24 na yaye daliban Jami’ar Maiduguri.
“’Yan ta’addan sun bude wuta kan ayarin motocin daga bangarori biyu, inda suka kashe dan sanda guda nan take, yayin da wata majiyar ta ce dayan kuma ya mutu daga baya sakamakon zubar jini da yawa saboda raunukan harsasai.
“Amma gaskiya mun bar Maiduguri a makare, sai wajen misalin karfe 5:40 na yamma,” in ji shi.
Sai dai Gwamna Buni ba ya cikin ayarin motocin a lokacin da lamarin ya faru kasancewar ya tafi Abuja ne domin gudanar da wani aiki.
Wannan dai shi ne karon farko da aka kai wa ayarin motocin gwamnan hari tun bayan barkewar rikicin Boko Haram shekaru 13 da suka gabata.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu cikakken bayani kan yawan wadanda aka kashe ko aka jikkata wa su ’yan ta’addan.